Majalisar wakilai ta yi kira da a samar da tsaro a fadin makarantun kasar nan domin magance tabarbarewar tsaro a kasar nan.
Matakin da majalisar ta dauka na biyo bayan amincewa da kudirin da Billy Osawaru ya gabatar a zauren majalisar a yau.
Da yake gabatar da kudirin, Osawaru ya nuna rashin jin dadinsa ta yadda dalibai ba su da kwanciyar hankali a makarantunsu, musamman a jihohin Borno da Nasarawa da Neja da Zamfara da Katsina da kuma Kaduna.
Dan majalisar ya ce, wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wasu dalibai kusan 24 na Jami’ar Tarayya ta Gusau a Jihar Zamfara.
Ya yi gargadin cewa za a iya rufe makarantu idan har aka ci gaba da kai hare-haren ta’addanci a makarantun kasar nan.
Dan majalisar ya kara da cewa a Najeriya ‘yan sanda ba sa gadin mafi akasarin makarantun duk da irin hare-haren da makarantun ke yawan fuskanta da kuma wadanda ake da su ba su wadatar da ma’aikata da kayan aiki ba, domin haka a duk lokacin da irin wadannan hare-hare suka afku kama ya yi su dauki mataki.
Osawaeu ya kuma ce, an kashe dalibai sama da 180, sannan kusan 90 sun jikkata a hare-hare 70 tsakanin watan Afrilun 2014 zuwa Disamba 2022, inda aka yi garkuwa da ma’aikatan makarantar kusan 60 sannan aka kashe 14. An kuma lalata gine-ginen makarantu 25 a wannan lokacin.
An yi garkuwa da kimanin ‘yan makaranta 287 daga wata makaranta mallakar gwamnati a garin Kuriga na jihar Kaduna.