Shugabannin Tarayyar Turai sun yi kiran a samar da “hanyoyin jin ƙai kuma a tsahirta” don ba da damar kai kayan agaji ga fararen hula a Gaza.
A cikin wani ƙuduri da suka ayyana yayin wani taro a Brussels, shugabannin ƙasashen Tarayyar Turai 27 sun bayyana “matuƙar damuwa saboda ƙazancewar al’amura a Gaza”.
Sun yi kira a “ci gaba kuma cikin hanzari a samar da amintacciyar hanyar jin kan ɗan’adam don kai kayan agaji ga waɗanda ke cikin tsananin buƙata ta hanyar ɗaukar dukkan matakan da suka wajaba ciki har da kafofin jin kai sannan a dakata don buƙatun ayyukan jin kai”.
Kudurin ya kuma ce Majalisar Turai “ta jaddada yin alla-wadai cikin murya mafi kaushi ga Hamas saboda hare-harenta na mugunta da ta’addanci a kan Isra’ila”.
Ta kuma kara da cewa: “Amfani da fararen hula a matsayin garkuwa da Hamas ke yi shi ma musamman aika-aika ne da ake yin tur da ita.”