Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi kira da a samar da sabon tsarin zaɓen shugaban hukumar zabe ta ƙasa (INEC), inda ya ba da shawarar kafa wani tsarin tantancewa da zaɓe mai zaman kansa don ƙara wa hukumar sahihanci kafin zaɓen gaba na 2027.
Jonathan ya bayyana wannan ra’ayi ne a ranar Laraba a Abuja, a yayin gabatar da shirin ƙasa na gyaran harkokin zaɓe, wanda Makarantar Nazarin Zamantakewa da Siyasa ta Abuja ta shirya.
Kiran ya zo ne a wani lokaci na siyasa mai ɗaukar hankali, yayin da wa’adin shugaban INEC na yanzu, Prof. Mahmood Yakubu, ke ƙarewa a watan Oktoba na wannan shekara.
Yakubu, wanda ya jagoranci zaɓukan 2019 da 2023, ya riga ya yi wa’adin aiki biyu, kuma zaɓen wanda zai gaje shi na janyo ƙarin hasashe a al’umma.
Masana na ganin cewa wanda zai zama sabon shugaban INEC zai taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da sahihancin zaɓen 2027.
Jonathan, wanda a baya an yi hasashen cewa zai iya komawa takarar shugaban ƙasa a 2027, ya ce; “Ina ganin Najeriya na iya inganta tsarin zaɓe ta hanyar kafa wani kwamitin tantancewa da zaɓe mai zaman kansa, wanda zai ƙunshi wakilai daga kotuna da ƙungiyoyin fararen hula jami’o’i da ƙungiyoyin da kwararru.”
“Wannan kwamitin zai tantance kuma ya bayar da jerin sunayen ‘yan takarar da ke neman shugabancin INEC da suka cancanta, daga cikinsu shugaban ƙasa zai iya zaɓa shugaban INEC ɗin.”
“Wannan zai rage tunanin son zuciya da ƙara amincewar jama’a da inganta sahihancin hukumar zaɓe INEC.” tsohon shugaban ƙasar ya ƙara da cewa