Hukumar kashe gobara da kai ɗaukin gaggawa ta jihar Legas, ta ce yanzu haka tana ƙoƙarin ceto wasu mata biyu da jariri waɗanda gini ya rufta ma wa a unguwar Ebuta Meta da ke birnin Ikko.
A cikin wata sanarwa da shugabar hukumar, Margaret Adeseye ta fitar a safiyar yau Juma’a, ta ce sun kai ɗaukin ne bayan samun kira na neman ɗauki daga wani gida a layin Herbert Macaulay Way a unguwar ta Ebuta Meta da misalin ƙarfe 9 na safe, inda aka sanar da su game da rugujewar ginin mai hawa ɗaya.
Yayin da ake ƙoƙarin aikin zaƙulo waɗanda suka rage ƙaƙashin ɓaraguzai, an samu nasarar ciro wata mace ɗaya wadda ba ta jigata ba


