fidelitybank

A na zargin mataimakin Kwamishinan Ƴan Sandan ya kashe kansa a Oyo

Date:

An gano gawar wani jami’in ɗan sanda mai muƙamin mataimakin kwamishinan ƴan sanda Gbolahan Olugbemiyashe a gidansa da ke Ogbomosho a jihar Oyo.

A cewar jaridun Najeriya, Olugbemi, da ke rundunar ƴan sanda ta jihar Legas, ya je hutu ne domin bikin ista inda ya gamu da ajalinsa.

Babban jami’in ɗan sandan wanda aka yaba masa saboda rawar da ya taka a zanga-zangar EndSars da aka yi domin nuna adawa da cin zalin jami’an tsaro, ya mutu ne a wani yanayi mai matuƙar ɗaure kai.

Mutuwar jami’in ta jefa abokan aikinsa da ke aiki a sashen binciken manyan laifuka cikin alhini.

Rundunar ƴan sanda ta bakin mai magana da yawun sashen binciken manyan laifuka, ASP Aminat Mayegun ta ce za a yi bincike kan mutuwar ta sa inda ta ce ba lalle bane a ce ya kashe kansa ne kamar yadda ake raɗe-raɗi.

Wata majiyar ƴan sanda ta ce za a gayyaci wasu domin su amsa tambayoyi game da lamarin. Cikinsu har da waɗanda suka fara ganin gawar tasa.

punch newspaper nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp