Rundunar ‘yansanda jihar Legas ta ce, ta ƙaddamar da bincike kan mutuwar wani matashi mai shekara19, da ake zargin ya mutu sakamakon dukan da mahaifinsa ya yi masa.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Benjamin Hundeyin, ya fitar ya ce rundunar ‘yan sanda ta karbi rahoton ƙorafin zargin mahaifin ranar Talata.
Ya ce mahaifn mai suna Olumide ya ji wa ɗan nasa, Adeyemi rauni sakamakon dukan da ya yi masa da shobel/tebur kan wani laifin da ba a bayyana ba.
Hundeyin ya ce matashin ya ji mummunan rauni a hannunsa sakamakon dukan.
“An garzaya da matashin zuwa asibiti don ba shi kulawar da ta dace, amma daga can sai aka tura su zuwa babban asibitin Ikeja sakamakon girman ciwon, inda a nan ne ya mutu sakamakon kamuwa da cutar tetanos, kamar yadda likitoci suka bayyana”, in ji sanarwar ‘yan sandan.
‘Yansanda sun ce tuni suka kama mahaifin domin gudanar da bincike.