fidelitybank

A na zanga-zangar tsadar rayuwa a Edo Osun

Date:

Mambobin ƙungiyoyi masu zaman kansu sun bazu kan tituna a jihohin Edo da Osun a ranar Litinin suna zanga-zanga kan tsadar rayuwa a Najeriya.

Hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar ya kai kashi 29 cikin ɗari, tun bayan janye tallafin mai ne rayuwa ke ƙara tsada.

Masu boren sun bazu kan tituna a Benin da Osogbo, manyan biranen jihar Edo da Osun da ke kudancin ƙasar.

A birnin Benin, masu zanga-zangar sun yi tattaki daga dandalin Kings zuwa titin Akpakpava, suna ɗauke da kwalaye waɗanda aka yi wa rubuce-rubuce kan batun tsadar rayuwa da ƴan ƙasar ke fuskanta da kuma buƙatar da ke akwai na magance matsalar yunwa a ƙasar.

A jihar ta Edo ɗan takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar hamayya ta NNPP a zaben da ke tafe a jihar, Dr Azemhe Azena na daga cikin waɗanda suka fito zanga-zangar, inda ya nemi gwamnati ta ɗauki matakan kawo ƙarshen tsadar rayuwa a ƙasar.

A birnin Osogbo na jihar Osun, masu boren sun yi gangami a wurin shaƙatawa na Nelson Mandela, inda su ma suka yi kira ga gwamnati da ta kawo ƙarshen tsadar rayuwa.

A baya-bayan nan an yi irin wannan zanga-zangar a wasu sassan ƙasar, kamar a jihohin Legas da Neja da birnin Ibadan na jihar Oyo da kuma jihar Kano.

nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp