A jiya ne Sarkin Muhammad na shida ya ayyana zaman makokin kwana uku a faɗin ƙasar.
Ya kuma bayar da umarnin kai taimakon tanti da abinci da sauran kayan agaji ga waɗanda suka tsira – sannan ya tura sojoji domin su taimaka wajen aikin ceto da ake ci gaba da yi.
An sauke tutocin ƙasar zuwa rabi a kusan duka gine-ginen ƙasar kamar yadda kamfanin dillancin labarai na ƙasar ya rawaito.
Sama da mutum 300,000 ne girgizar ƙasa ta shafa a Marrakesh da ƙauyukan da ke gefen garin a Morocco, kamar yadda ofishin jinƙai na Majalisar Ɗinkin Duniya ya bayyana.
Rahotanni sun ce ofishin na “bibiyar abubuwan da suke faruwa a Morocco sau da ƙafa kuma a shirye yake ya kai ɗauki”.
A wata sanarwa da ya fitar tun da fari ya ce, MDD ta ce a shirye take ta taimakawa gwamnatin Morocco a ƙoƙarin da take na shawo kan lamarin.


