Ana cikin zaman takaici a Awka babban birnin jihar Anambra.
Jihar ta kasance mahaifar ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar Labour Peter Obi, wanda ya zo na uku a zaɓen da aka kammala.
A’amura sun koma yadda suke yayin da mutane ke ci gaba da harkokinsu a jihar da Mista Obi wanda ya kasance hamshakin ɗan kasuwa, ya yi mulki a matsayin gwamna har sau biyu.
Amma idan ka duba, za ka gansu cikin bakin-ciki kan sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar a ranar Asabar.
Mutane da dama da aka tattauna da su, sun nuna suna cikin ɓacin-rai – kamar hukumar zaɓe ta ƙwace musu kuri’unsu, zaɓe kuma da suka ce yana cike da kura-kurai.