An buɗe rumfunan zaɓe a babban zaɓen Birtaniya, inda miliyoyin masu kaɗa ƙuri’a ke zaben ƴan majalisa, da kuma sabon Firaminista.
Dole ne masu zaɓe su gabatar da katinsu na shaida kafin kaɗa ƙuri’a a rumfunan zaɓe.
Za a rufe rumfunan ne da ƙarfe 10 na dare agogon ƙasar da kuma na Najeriya, inda a lokacin ne kuma ake sa ran sakin sakamakon farko.
BBC ba ta da damar kawo maku rahotannin yaƙin neman zaɓe ko na siyasa da suka danganci zaɓen yayin da ake gudanar da shi, to amma za mu rika kawo muku bayanai daga rumfunan zaɓen da kuma yadda abubuwa ke gudana.