Rundunar sojin ƙasa, a ranar Laraba, ta musanta wani rahoto da ke cewa, wasu jami’an da ke aiki na shirin kutsawa Abuja, domin nuna adawa da rashin biyansu albashi da kuma rashin kyakkyawan yanayin aiki.
Onyema Nwachukwu, Birgediya Janar, Daraktan Hulda da Jama’a na rundunar a cikin wata sanarwa ya bayyana rahotannin a matsayin marasa tushe da kuma yunkurin wasu makiya marasa fuska na tozarta sunan sojojin.
Ya ce, jami’ai da ma’aikatar sun shaida sauye-sauye masu kyau a bangaren dabi’u da na jiki na rundunar.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, rundunar sojojin ƙasa a karkashin jagorancin mai ci ta ba wa jami’ai da maza daman aiki tukuru, wanda hakan ya sa su yi aiki tukuru da dukkan kayan aikin da aka cusa musu.