fidelitybank

A na tuhumar Rasha da kashe Fararen hula dagaske a Ukraine

Date:

Wasu hotuna da suka karaɗe duniya na nuna yadda sojojin Rasha ke harbin wani mutum yayin da hannayensa ke ɗage a sama kan wata babbar hanya da ke wajen birnin Kyiv a farkon watan Maris.

An kori sojojin Rasha daga yankin bayan mamayar da suka yi masa na wani ɗan lokaci.

Mun kirga gawarwakin mutum 13 akan wata hanya mai ban tsoro da ba ta wuce mita 200 ba tsakanin Mria da Myla, ƙauyukan da sunayensu ke nufin Buri da Sanyin Zuciya harshen Ukrane, ko kuma Dream and Sweetheart a Turance.

Biyu daga cikin wadanda aka kashe an tabbatar da fararen hular Ukraine ne, wadanda sojojin Rasha suka kashe. Amma har yanzu ba a tantance sauran ba, suna kwance a inda aka kashe su, sai dai biyu daga cikinsu ne kawai ke sanye da kakin sojin Ukraine.

Tawagar BBC ta samu damar zuwa inda lamarin ya faru a kan babbar hanyar E-40 zuwa birnin Kyiv, saboda sojojin Ukraine sunƙwace yankin ne cikin sa’o’i 10 kacal da suka wuce.

Akwai alamomin yaki da luguden wuta a ko’ina a yankin. Gidajen mai da wani hotel da ya yi fice wajen shakatawa da gidajen abinci sun kasance a ɗaiɗaice. Luguden wuta ya bar alamomi a kan hanyoyin biyu.

An bar gawarwakin cikin wani hali na rashin kulawa, akwai alamar, tambayoyi da damuwa game da ko su wane ne su da kuma yadda suka mutu.

legit breaking news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp