fidelitybank

A na ta cece-kuce a jam’iyyar PDP bayan kowa ya dakatar da kowa

Date:

Rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar PDP ya ɗauki sabon salo bayan ɓangarori biyu sun dakatar da junansu daga jam’iyyar.

Ɓangaren shugaban jam’iyyar na riƙo, Umar Damagun ya dakatar da sakataren watsa labarai na jam’iyyar Dabo Ologunagba, da mai ba jam’iyyar shawara a kan harkokin shari’a, Kamaldeen Adeyemi Ajibade, SAN daga jam’iyyar, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ana cikin haka ne ɗayan ɓangaren suka fitar da tasu sanarwar, inda suka ce sun dakatar da Umar Damagun da sakataren jam’iyyar, Samuel Anyanwu daga jam’iyyar.

Chinwe Nnorom, daraktan watsa labarai a hedkwatar jam’iyyar ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis, inda ta ce “bayan taron majalisar zartarwa na jam’iyyar na 59, an dakatar da sakataren watsa labarai na jam’iyyar, Debo Ologunagba da mai ba da shawara kan harkokin shari’a, Kamaldeen Adeyemi Ajibade SAN daga aiki, sannan an umarci mataimakansu su cigaba da ayyukansu.”

Wannan wani sabon babi ne a rikicin babbar jam’iyyar adawar a kan shugabanci wanda aka daɗe ana yi.

general news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp