Gwamnan Imo kuma ɗan takarar jam’iyyar APC, Hope Uzodimma, ya lashe dukkan ƙananan hukumomin jihar 27 a zaɓen gwamnan da aka gudanar ranar Asabar.
Babban Baturen Zaɓe Farfesa Abayomi Fashina na Tarayya ta Oye Ekiti ne ke jagoran tattara sakamakon kuma a kowane lokaci nan gaba kaɗan zai iya bayyana wanda ya yi nasara a zaɓen.
Zuwa yanzu APC na da ƙuri’a 540,308, sai kuma PDP mai ƙuri’u 71,503, da kuma Labour Party mai ƙuri’u 64,081.
Tun da misalin ƙarfe 2:00 na dare ranar Asabar aka fara tattara sakamakon zaɓen, wanda ake ganin ya tafi lafiya ƙalau a mafi yawan rumfunan zaɓe duk da faragabar tashin hankali da aka rinƙa yi sakamakkon ayyukan ‘yan bindiga a jihar.