A Birtaniya za a fara bikin kwanaki hudu, domin taya Sarauniya Elizabeth murnar kafa tarihin shekaru 70 kan karagar mulki.
Ana sa ran miliyoyin mutane za su halarci gagarumin bikin, da ya hada da dab-dala a tituna, inda makadan badujala za su cashe, za kuma ayi fareti kala-kala da harbin bindigar girmamawa.
Wakilin BBC ya ce, abu ne da ba a saba gani ba a bikin cika shekara 70 kan karaga a kasashen rainon Ingila na Commonwealth, wato kunna fitila a gini mafi tsaho da karfe 9 da kwata na dare.
Ana sa ran kasashe 54 da ke cikin commonwealth za su halarci bikin.
Za a fara kunna wutar daga Samoa da Tonga a kudancin Pacific.