A wasu wuraren an fara tattara sakamakon zaɓe, kamar na Sanatan Kano ta arewa wato a yankin Bichi.
Sai dai wasu wuraren kuma har zuwa safiyar Lahadi ana jira ne saboda sakamakon bai haɗu ba daga matakin cibiyoyi zuwa kananan hukumomi.
Haka shi ma sakamakon zaben shugaban ƙasa ana sa ran farawa a yau.
An samu jinkirin ne saboda jiya wasu wuraren ba a fara kada kuri’a a kan lokaci ba sannan na’urar tantance masu kada ƙuri’a ta VBAS ba ta yi aiki yadda ya kamata ba a wurare da dama sannan an ɗan samu yamutsi nan da can.