Kundin bajinta na Guinness World Records, ya ce ya lura ana samun ƙaruwar yunƙurin kafa tarihin bajintar daga ƙasashen yammacin Afirka.
A ƴan shekarun nan, dubban ƴan Afirka musamman daga Najeriya na aika buƙatar shiga wannan fage, cikin abubuwan da aka fi son kafa tarihin akwai girke-girke, da gabatar da jawabi mafi tsawo da fannin ƙwallon ƙafa.
Yawancin masu son kafa tarihin sun samu ƙwarin gwiwa ne bayan matashiyar mai girkin ƴar Najeriya, Hilda Baci, ta samu nasarar kafa tarihin mafi daɗewa ana girka abinci.
Fitattun mutane da ƴan siyasa da miliyoyin ƴan Najeriya a shafukan sada zumunta ne suka ƙarfafa mata gwiwa a lokacin da ta ke girkin har ta kai ga samun nasara.