Isra’ila ta ce tana sa ran sakin karin mutum 13 daga cikin wadanda Hamas ke garkuwa da su a yau.
Haka kuma ana sa ran ita ma Isra’ila ta saki karin Falasdinawa masu yawa da take tsare da su a gidajen yarinta.
Sannan kuma, akwai manyan motoci makare da kayan agaji da ke jiran a tantance su a kan iyakar Rafah domin shiga Gaza.
Duk da cewa yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Hamas da Isra’ila karkashin jagorancin Qatar domin kawo karshen yakin, rahotonni na cewa har yanzu akwai tsananin bukatar kayan tallafi a Gaza.
Akwai rahotonnin karancin man fetur da abinci da ruwan sha da magunguna da kayan aiki.
Kusan motocin agaji 200 ne suka shiga Gaza a ranar Juma’a, adadi mafi yawa tun ranar 26 ga watan Satumba.