fidelitybank

A na nuna mana wariyar kalar fata a kan iyakar Ukraine – ‘Yan Afrika

Date:

‘Yan Afirka da ke kokarin tsere wa daga Ukraine na ƙorafin fuskantar wariya a kan iyakokin Ukraine zuwa cikin Tarayyar Turai.

Wata daliba ƴar Najeriya da ke karatun likitancia wata jami’a a Kharkiv, ta ce yi tafiya na tsawon sa’a 11 cikin dare kafin ta isa Medyka-Shehyni, da ke kan iyaka da Poland.

“Lokacin da na zo nan na ga baƙaƙen fata suna bacci kan titi,” kamar yadda ta shaida wa wakiliyar BBC.

Ta ce jami’an tsaron kan iyaka sun shaida mata cewa ta jira har dai ƴan Ukraine sun wuce sannan. Ba ta iya tantance ko masu gadin kan iyakar na Ukraine ne ko kuma Poland.

Ta ce ta ga an cika motocin bas da mutane waɗanda ta bayyana fararen fata, da aka amince su tsallaka kan iyaka, yayin da kuma ake zaɓen baƙaƙen fata da suka yi layi suna jiran tsammani.

Ruqayya na ƙoƙarin shiga Warsaw ne domin samun jirgin da zai dawo da ita gida Najeriya.

Isaac ya ce, ya wuraren ƙarfe 4.30 na safe ya isa kan iyakar Medyba kuma ya ce an faɗa masa cewa sai ƴan Ukraine da ƴan Turkiya sun wuce kafin baƙaƙen fata.

Jami’an kula da kan iyakokin Poland sun ce suna barin duk wanda ya fito daga Ukraine shiga ƙasar.

Ofishin jakadancin Najeriya a Poland ya ce, ya tura jami’ansa zuwa kan iyakoki, domin taimakawa ƴan ƙasar tsallakawa.

punch news paper today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...

A sake sabon tsarin shugabancin INEC a Najeriya – Goodluck

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi kira da...

Magoya bayan West Ham ku hada kai da Bowen – Potter

Mai horas da West Ham, Graham Potter ya bukaci...

Alhaki na ne kifewar jirgin kasa – Shugaban Hukumar

Shugaban hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC), Kayode Opeifa,...
X whatsapp