Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya yi kira ga jama’a da su kai ɗaukin jini yayin da jami’an lafiya ke ƙoƙarin kula da waɗanda suka jikkata sanadiyyar haɗarin jirgin ƙasa a yau Alhamis.
Cikin saƙonnin da ya wallafa a shafinsa na Tuwita game da haɗarin, Mista Sanwo-Olu ya ce, har yanzu wasu da lamarin ya shafa suna cikin wani yanayi.
Karanta Wannan: Mun samu korafe-korafe 246 a Kano – Hukumar Kare Hakki
Ya ce motar bas ɗin na ɗauke da ma’aikata 85 ne a lokacin da ta yi taho mu gama da jirgin a Ikeja.
Gwamnan ya tabbatar da mutuwar mutum shida inda ya ce wasu 29 kuma rai na a hannun Allah. Wasu 42 kuma sun ɗan jikkata sai ƙarin wasu takwas da suka kukkurje.
Ya yaba wa ma’aikatan agaji da sauran waɗanda suka sa hannu a aikin agajin da kuma ma’aikata da ɗaliban asibitin koyarwa na Jami’ar Legas inda ake kula da waɗanda suka ji rauni.