A na ci gaba da ayyukan ceto bayan ambaliyar ruwan da ta auku a garin Mokawa na jihar Neja, inda ya zuwa yanzu aka gano sama da gawa 150, kuma akwai sauran fiye da 400 da ake nema, yayin da gwamnatin jihar Neja da hukumomi da kungiyoyin agaji ke ci gaba da kai dauki ga daruruwan mutane da ambaliyar ruwan ta shafa.
Kwamared Yakubu Garba, mataimakin gwamnan jihar Nejar, wanda ya kai ziyarar gani da ido da kuma jaje garin na Mokwa ne ya bayyana wa BBC hakan, inda ya ce lamarin akwai ɗaga hankali.
Ya ce, “Aƙalla akwai mutum 40 ba suka ɓace har yanzu ba a gansu ba kuma ba a gano gawarsu ba. Ana dai cigaba da nemansu.”