Ƙungiyar kare haƙƙin yara ta Save the Children,reshen Falasɗinu ta ce ana kashe yaro ɗaya cikin kowane minti 10 sakamakon yaƙin da Isra’ila ke yi a Zirin Gaza.
Da yake magana da BBC daga birnin Ƙudus, shugaban ƙungiyar Jason Lee ya ce baya ga yara 20,000 da aka jikkata, ɗaya cikin duk mutum uku yaro ne.
Ya ce cutuka masu yaɗuwa na ƙaruwa saboda cunkokso da kuma ƙarancin kayan tsafta.
“Likitoci na yin tiyata ba tare da yi wa mutane allurar kashe zafin ciwo ba, mutane na amfani da wayoyinsu don ganin haske a asibitoci,” in ji shi.