An samu arangama mai ƙarfi tsakanin dakarun sojin Sudan da rundunar mayaƙan RSF, a kusa da sansanin soji da ke birnin Khartoum na ƙasar Sudan.
Cikin wata sanarwa da sojojin suka wallafa a shafinsu na Facebook ranar talata da daddare, sun ce sun daƙile wani hari da RSF suka kai sansanin soji da ke yankin Al-Shajara a kudancin birnin Khartoum.
Sojojin sun kuma yi iƙirarin kashe da yawa daga cikin mayaƙan RSF ɗin.
A nata ɓangare, mayaƙan na RSF sun ce sun ƙwace iko da wasu yankuna a sansanin tare da kama makamai masu dinbim yawa, cikin wata sanarwa da suka fitar a shafinsu na X da a baya aka fi sani da Twitter.
Gidan talbijin na Al Arabiyya – da ƙasar Saudiyya ke ɗaukar nauyinsa – ya ce har yanzu sojojin ne ke iko da sansanin bayan kwashe kwana uku ana gwabza faɗa a sansanin.
A ‘yan kwanakin nan faɗa na ci gaba da rincaɓewa a birnin Khartoum da biranen Omdurman da Bahri da wasu yankunan yankin Darfur.
Majalisar Dikin Duniya ta ce dubban mutane ne suka mutu, yayin da aka raba da sama da mutum miliyan huɗu da muhallansu tun bayan ɓarkewar yaƙi tsakanin sojoji da dakarun RSF a tsakiyar watan Afrilu


