Faɗa na ci gaba da rincaɓewa a birnin Gaza, kuma kamar yadda muka ruwaito tun da farko, ɗafa na ci gaba da tsananta a kusa da asibitin Al Quds yayin tankokin yaƙi ke tunƙarar asibitin.
Hanyoyin sadarwa sun yi wahalar gaske, to amma na samu zanta wa da wani mutum da safiyar nan, wanda ya ce faɗa ya tsananta a yankin.
Sojojin Isr’aila sun kai wa gine-gine da dama hari a yunƙurinsu na mayar da martani kan harin ranar 7 ga watan Oktoba da Hamas ta kai Isra’ila.
An kwashe kwanaki ana kai hare-hare ta sama a yankin. A yanzu ana kai hare-hare wurin daga cikin teku da ta ƙasa.