fidelitybank

A na gudanar da addu’ar cika shekaru 73 da haihuwar Tinubu

Date:

Za a gudanar da wata addu’a ta mausamman ga Najeriya yau Juma’a a babban masallacin ƙasa da ke Abuja, a matsayin wani ɓangare na murnar cikar shugaban ƙasar shekara 73 da haihuwa.

Fadar shugaban ƙasar ce ta sanar da haka a cikin wata sanarwa da mai bashi shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga ya fitar.

Sanarwar ta ce Tinubu zai haɗu da al’umma Musulmi a massalacin a yau Juma’a domin addu’ar, domin zagayowar ranar haihuwarsa wadda za ta kasance gobe Asabar 29 ga watan Maris.

Sanarwar ta ce za a yi amfani da damar wajen yin godiya ga Allah da ya ba shi tsawon rai kuma yake taimakasa gudanar da gagarumin aikin jagorantar Najeriya.

Sanarwar ta ce shugaba “Tinubu ya yi imanin cewa gabatar da addu’o’i a matsayin ƙasa ɗaya wani babban abu ne dai zai taimaka wajen kai ƙasar ga ci gaba da zaman lafiya.”

Tinubu ya kuma buƙaci ɗaukacin al’ummar musulmi su yi addu’oi’n ga ƙasar a duk inda suke.

Shugaban ƙasar ya kuma miƙa godiyarsa ga ƴan Najeriya bisa goyon bayan da suke ba gwamnatinsa a ƙoƙarin da yake yi ba dare ba rana wajen bunƙasa tattalin arziƙi da inganta tsaro da kuma faɗaɗa samun damarmaki ga ƴan ƙasar.

Ya ce ” ina matuƙar godiya ga Allah na rayuwar da ya ba ni damar hidimtawa Najeriya. A yayin da nake murnar zagoyowar ranar haihuwata, zuciyata a cike take da sabuwar fata ga Najeriya. Ina buƙatar ƴan Najeriya su yi addu’a, da haɗin kansu zamu shawo kan matsalolinmu kuma mu gina ƙasar da kowa zai amfana’.”

Tinubu ya kawo sauye-sauye da dama a ɓangaren tattalin arziƙin ƙasar tun bayan hawan sa kan mulki a shekara 2023, sai dai al’ummar ƙasar na kokawa kan yadda tsare-tsaren gwamnatin ke jefa su cikin ƙunci, sanadiyyar tashin farashin kayan masarufi da kuma talauci

nigeria 
news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp