Shalkwatar tsaro ta bayyana hare-haren bam na baya-bayan nan da aka kai jihar Borno a matsayin wani yanayi da ya mayar da ƙasar cikin yanayin yaƙi.
Bayanin hakan na ƙunshe cikin wata sanarwar da daraktan yaɗa labarai na hedikwatar tsaron, Manjo Janar Edward Buba ya fitar ranar Talata.
Manjo Janar Buba ya bayyana cewa hari na farko a ranar Asabar ya faru da ƙarfe 3:00 na rana lokacin da wata ƴar ƙunar baƙin wake da ta yi bad-da-kama a matsayin mabaraciya ta durfafi wani wajen biki a unguwar Mararaba Hausari tare da ta da abin fashewa.
Sai dai bayan nan da ƙarfe 5 na yammacin ranar yayin da ake ƙoƙarin kwashe mutanen da suka jikkata sakamakon harin farko zuwa asibiti domin samun kulawa, aka sake samun wata da ta sake ta da abin fashewa kusa da inda lamarin farko ya afku.
A cewar Buba, sojoji nan da nan suka ayyana dokar hana fita a garin domin hana zirga-zirga.
Sai dai a yayin da sojojin da sauran jami’an tsaro ke tabbatar da dokar hana fitar ne kuma aka sake samun wani abin fashewar da ya tashi.
Ya ce “Hari na uku ya shafi sojoji da ke koƙarin tabbatar da dokar hana fita. Wata matar ce kuma ta kai harin lamarin da ya halaka soji guda da kuma wasu jami’an tsaro biyu.
“Hari na huɗu kuma, an daƙile shi lokacin da wadda ake zargi ta ta da bom da ya yi ajalinta. A jumulla, mutum 20 ne suka mutu yayin da 52 suka ji rauni kma suna jinya a asibiti.” in ji sanarwar.
Hedikwatar tsaron ta ƙara da cewa mayaƙan sun kai hare-haren ne kan mutanen da ba su ji ba su gani ba domin nuna cewa suna nan da ƙarfinsu.
“Rundunar soji tana sane da cewa mayaƙan na son karkato da hankali gare su, su kuma rage goyon bayan da ake bai wa sojoji da kuma gwamnati.”
Kan haka ne rundunar ta yi kira ga al’umma da su ci gba da haɗa kai su kuma yi taka tsan-tsan tare da ƙara tallafa wa ƙoƙarin dakarun ƙasar domin tabbatar da tsaron rayuka a ƙasar.