Hukumomi sun ce kasar nan na fuskantar barazanar barkewar cutar Ebola, da ake tunanin shigo da ita daga kasar Uganda.
Hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta kasar NCDC ta ce an samu karuwar baranazar barkewar cutar ne sakamakon yawan zirga-zirgar fasinjoji da aka yi tsakanin Najeriya da Uganda, da kuma cudanyar fasinjoji, musamman a filayen jiragen sama na Nairobi, da na Addis Ababa, da kuma filin jirgin sama na Kigali.
Hukumomin lafiyar kasar sun ce suna cikin shirin ko ta kwana, yayin da suka dauki matakan da suka dace domin yakar cutar idan ta barke.
Matakan sun hada da sanya ido kan fasinjoji tare da tantance su a filayen jiragen saman kasar.
Hukumar ta shawarci ‘yan kasar da su guji yin tafiye-tafiye zuwa Uganda idan ba ta zama dole ba, daga yanzu zuwa wasu lokuta.
NCDC ta ce fasinjojin da suka zo kasar daga Uganda za a sanya ido a kansu na tsawon mako uku, domin tabbatar da halin da suke ciki.
An samu bullar cutar a kan mutum 100 tare da mutuwar mutum 30 a Uganda, tun bayan barkewarta a watan Satumba, ana kuma fargabar cewa cutar ka iya yaduwa zuwa makwabtan kasashe.