Mutum akalla 21 ne ake fargabar sun mutu a safiyar ranar Asabar yayin wani turmutsitsi a wata coci a Fatakwal da ke jihar Rivers.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa lamarin ya faru ne lokacin raba kyautuka da abinci kashi na hudu a harabar wurin.
Wanda lamarin ya fara a kan idanunsu sun ce wasu da aka gayyata suna cikin harabar wurin tun ranar Juma’a wasu kuma sun isa wurin ne da misalin karfe 6:30 na safiyar Asabar, a taron da aka tsara yi karfe 9 na safe.
Sun kara da cewa wasu da za su yi wani atisaye na wasanni ne suka zo da misalin karfe 8 suka bi ta karamar kofar shiga wanda daga nan ne kuma mutane suka samu damar fara kutsawa har yakai ga wannan turmustitsi.