A na fargabar Mutane biyu ne suka mutu sakamakon wata arangama da aka yi tsakanin rundunar ‘yan sanda da masu zanga-zangar ‘yan Shi’a a kasuwar Wuse da ke unguwar Wuse Zone 6 a babban birnin tarayya Abuja.
DAILLY POST ta rawaito cewa, rikicin ya yi sanadiyar zubar da jini lokacin da ‘yan sanda suka yi amfani da barkonon tsohuwa kan masu zanga-zangar.
Hotunan bidiyo sun nuna cewa masu zanga-zangar sun kai hari ofishin ‘yan sandan Kasuwar Wuse.
Har yanzu dai rundunar ‘yan sandan ba ta mayar da martani ga ci gaban da aka samu ba har zuwa lokacin gabatar da rahoton.