Ana fargabar mutane da dama sun mutu wasu kuma sun ɓata a Yaounde babban birnin Kamaru, bayan wata zaizayar ƙasa da aka yi da ta lalata gidaje da yawa a yanki Mbankolo.
Wannan na zuwa bayan wani ruwan sama da aka yi kamar da bakin kwarya a ranar Lahadi.
Kafafen yaɗa labarai na Kamaru na ruwaito cewa mutum 13 sun mutu yayin wannan masifa, kuma ana tsammanin adadin ka iya ƙaruwa nan da wani lokaci.
masu aikin ceto na ta kai-kawo a yankin, kuma har yanzu ba a san adadin mutanen da abin ya rutsa da su ba.
A watan Nuwambar bara, an samu irin wannan zabtarewar ƙasa a babban birnin Kamaru, abin da ya janyo mutuwar mutum 14.
A ranar Lahadi a makwabciyar ƙasar Najeriya, an yi gargaɗin za a iya samun irin wannan ambaliya a ƙasar.