A yau lahadi an ci gaba da kaɗa ƙuri’a a zaɓen gwamna da na ‘yan majalisaun dokokin jihohi a mazaɓar VGC a jihar Legas.
Hukumar zaɓen ƙasar ce ta ce za a gudanar da zaɓen ne a yau kasancewar ba a samu gudanar da zaɓen a irin waɗannan mazaɓu ba.
A sanarwar da hukumar INEC ta fitar ta ce, ba a samu gudanar da zaɓen a wannan mazaɓa ba kasancewar masu kaɗa ƙuri’a sun turje wa ma’aikatan da aka tura.