Kano na ɗaya daga cikin jhihohin da ake kaɗa ƙuri’a a zaɓen cike gurbi da hukumar zaɓe ta Najeriya ke gudanarwa a yau Asabar.
A Kanon, za a fafata zaɓen ne kan kujerun ‘yanmajalisa na mazaɓun ƙananan hukumomin Bagwai da Shanono da Ghari da Tsanyawa duka a majalisar jihar.
Masu zaɓe na can na kaɗa ƙuri’unsu a zaɓen cike gurbi a wasu jihohin Najeriya.
A waɗannan hotunan, ma’aikatan hukumar zaɓe ta Independent National Elrctoral Commission (Inec) ne ke tantance masu kaɗa ƙuri’a kafin ba su damar yin zaɓen a Mazaɓar Isekke da ke ƙaramar hukumar Ihiala ta jihar Anambra.