fidelitybank

A na cigaba da farautar Fursunonin Osun da suka tsere

Date:

Hukumar gyaran hali ta Najeriya (NCoS) ta ce, ta ƙaddamar da bincike tare da farauta mai zurfi domin kama fursunoni bakwai da suka tsere daga gidan gyaran hali da ke Ilesa a Jihar Osun, bayan ruwan sama mai ƙarfi da ya lalata tsaron wurin.

Mai magana da yawun hukumar, Umar Abubakar, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar da daren Talata.

Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 2 na dare, a ranar Talata, 20 ga watan Mayun 2025, inda hakan ya haifar da tserewar fursunoni bakwai.

“Biyo bayan faruwar lamarin, shugaban hukumar gyaran hali na ƙasa, Sylvester Ndidi Nwakuche, ya bayar da umarnin gaggauta gudanar da bincike kan yadda fursunonin suka samu damar tserewa,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta ƙara da cewa hukumar tana aiki kafada da kafada da sauran hukumomin tsaro da shugabannin al’umma domin kamo waɗanda suka tsere tare da mayar da su gidan yari.

Hukumar ta kuma nemi haɗin kai da goyon bayan jama’a wajen bayar da duk wata bayani da zai iya taimakawa wajen kamo waɗanda suka tsere.

nnn news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...

A sake sabon tsarin shugabancin INEC a Najeriya – Goodluck

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi kira da...

Magoya bayan West Ham ku hada kai da Bowen – Potter

Mai horas da West Ham, Graham Potter ya bukaci...

Alhaki na ne kifewar jirgin kasa – Shugaban Hukumar

Shugaban hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC), Kayode Opeifa,...
X whatsapp