Hukumomi a jihar Neja na ci gaba da gudanar da bincike kan sauran gawarwakin da ake tsammanin har yanzu suna cikin ruwan da wani kwale-kwale ya kife a ranar Lahadi.
Haɗarin ya faru ne a yankin Gbajibo na Ƙaramar Hukumar Mokwa a jihar Neja da ke arewacin Najeriya.
Malam Jibrin Abdullahi Murege shi ne Shugaban Ƙaramar Hukumar ta Mokwa wanda ya ce ya zuwa yanzu mutum 26 sun mutu, yayin da aka ceto sama da mutum 40, cikin kimanin mutum 100 da ke cikin jirgin.
Mahukunta sun ce mata manoma da yara ƙanana ne kawai a cikin jirgin, kuma suna ci gaba da gudanar da bincike domin tabbatar da an gano yawan adadin mutanen da rahotanni suka ce suna cikin jirgin.
Haɗarin jirgin ya faru ne sakamakon wani ice da jirgin ya daka a tsakiyar ruwa, wanda mahukunta suka ce an yanke shi ne a baya amma damuna ta sa ya ƙara toho kuma ba a iya ganinsa.
Kifewar jirgin ruwa a jihar Neja ba baƙon abu ba ne, ko wata uku baya sai da aka samu irin wannan kifewar jirgi mai ɗauke da mutane sama da 100 da suke kan hanyarsu ta dawowa daga gidan biki.
A wani labarin mai kama da wannan, wani jirgin ruwan ya kife a jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya ɗauke da mutum 23 a ranar Juma’a.
Rahotanni sun ce mutum 15 sun mutu waɗanda yawancin su manoma ne da ‘yan kasuwa da ke tare da ƙananan yara.
Haɗarin ya faru ne a kan hanyarsu ta zuwa birnin Yola daga ƙauyen Rugange da ke Ƙaramar Hukumar Yola ta Kudu.
An gano gawarwaki huɗu a lokacin da abin ya faru, sanadin masu aikin ceto da kuma masu ninƙaya na gargajiya.
Wani wanda abin ya faru a kan idanunsa ya ce, wata iska ce mai ƙarfi ta janyo faɗuwar jirgin.


