A ranar Juma’ar nan ne al’ummar Musulmi a wasu kasashen duniya ke bikin Sallar Azumi bayan kammala azumin watan Ramadana da ya kasance mai kwana 29.
Hukumomin Saudiyya sanar da ganin watan Shawwal da yammacin Alhamis wanda hakan ya kasance karshen watan Ramadan ke nan.
Sannan Najeriya da Nijar da kuma wasu kasashe su ma suka bi sahun Saudiyyar wajen sanar da ganin watan na Shawwal a ranar Alhamis.
To sai dai yayin da wadannan kasashe da ma wasu suke yin Sallar Idin Azumin a ranar Juma’ar nan, hukumomin Iran su kuwa sun ce sai ranar Asabar za a yi Sallar a kasar saboda ba su ga watan na Shawwal ba. In ji BBC.


