A Najeriya manyan mutane na ci gaba da nuna alhininsu kan rasuwar shugaban bankin Access na Najeriya, Herbert Wigwe wanda ya rasu a Amurka sakamakon hatsarin jirgi mai saukar ungulu da yake ciki tare da iyalansa.
Mista Wigwe tare da matarsa da kuma ɗansa sun rasa rayukansa ne a cikin hatsarin jirgin saman mai saukar ungulu a ranar Juma’ar da ta gabata a Amurka .
Jagoran adawa Atiku Abubakar ya aike da saƙon ta’aziyyarsa ga kan rasuwar mutumin da ya bayyana da fasihin mutum mai halin kirki da dattaku.
Cikin saƙon ta’aziyyar da ya wallafa a shafnsa na X, tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce ya kadu matuƙa da labarin rasuwar mista Wigwe, wanda ko yaushe burinsa shi ne tunanin kawo ci gaba.
Ita ma shugabar ƙungiyar kasuwanci ta duniya, Ngozi Okonjo Iweala, ta bayyana mutuwar Mista Wigwe mai shekara 57 da matarasa da dansa a matsayin babban rashi ga Najeriya baki ɗaya.
Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani a nasa ɓangare ya bayyana marigayin da cewa ɗaya ne daga cikin mutanen da ke da fikirar ɓullo da sabbani abubuwa
Tuni dai masu bincike a California suka fara bincike kan abin da ya janyo hatsarin jirgin.
Haka kuma wasu mutane uku da ke ciki jirgin suma sun mutu yayin da jirgin ya fado a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa garin Boulder daga Palm Springs a jihar Nevada.
Rahotonni na cewa an samu yanayi mara kyau tare da ruwan sama da zubar dusar ƙanƙara a yankin.