Rundunar Tsaron Isra’ila wato IDF ta ce ta kashe mambobin Hezbollah guda 250 a cikin kwana huɗun da suka gabata.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da IDF ɗin ta fitar, inda ta ce, “a kwana huɗu da suka gabata, IDF ta kashe ƴan Hezbollah 250, daga cikin su guda 21 kwamandoji ne,” kamar yadda sanarwar ta nuna.
Sanarwar ta ƙara da cewa sun kai hare-hare a wuraren mayaƙan ƙungiyar sama da 2,000, inda ta ce sun yi mayar da hankalinsu a kan kudancin Lebanon.