Fafaroma Francis, ya yi kira da a dauki kwararan matakai na kawo karshen yakin da ake a Ukraine da kuma kaucewa fada wa masifar nukiliya a Zaporizhzhia.
Da ya ke jawabi a yayin taron mako-makon da yake da mabiyansa, Fafaroman ya yi alawadai da yakin da ya kira rashin hankali, da kuma bayyana kisan da aka yi wa Darya Dugina, a matsayin rashin imani.
Fafaroman ya ce yana so ya kai ziyara Kyiv to amma yana so ya fara zuwa Moscow ne da farko don kawo karshen yakin