Mutum biyar da ake zargi da shirya harin bam a Coci Katolika ta Saint Francis da ke Owo, Jihar Ondo, a shekarar 2022, sun musanta tuhume-tuhume tara na ta’addanci da gwamnatin Tarayya ta shigar a kansu.
An gurfanar da su a gaban Mai Shari’a Emeka Nwite na babbar kotun tarayya a ranar Litinin, inda ake zargin su da kasancewa mambobin ƙungiyar ta’addanci ta Al-Shabab a sashenta na jihar Kogi, kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.
Mai Shari’a Nwite ya sanya ranar 19 ga Agusta, 2025 a matsayin ranar fara sauraron shari’ar, sannan ya yi umarni da a ci gaba da tsare su a hannun hukumar tsaro ta DSS.
Gurfanar na zuwa ne bayan shekara uku da tsohon babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Lucky Irabor, ya sanar da cewa an kama waɗanda ake zargi da kitsa harin.
Majalisar tsaro ta ƙasa ta danganta harin da miyagun ayyukan ƙungiyar ta’addanci ta ISWAP.
Fiye da mutum 40 ne suka rasu a harin, sannan da da dama suka jikkata, lokacin da ƴanbindigar suka kai farmaki a cocin a wata ranar Lahadi a daidai lokacin da suka gudanar da ibada.
Tsohon gwamnan Jihar, marigayi Rotimi Akeredolu, ya bayyana harin a matsayin “cin zarafin ɗan’adam.”