A ranar Juma’a ne yarima Harry da mai ɗakinsa Meghan Markle – masu riƙe da sarautar Duke da Duchess na Sussex na Birtaniya, ke wata ziyara ta yini uku a Najeriya.
Ma’auratan za su je Najeriya – a karon farko – bisa gayyatar da suka samu daga babban hafsan tsaron ƙsar Janar Chritopher Musa.
Ana sa rai za su kai ziyara wata cibiyar gyaran hali tare da ganawa da ƙungiyoyi da ke aiki domin tallafawa walwalar ƴan mazan jiya.
A yayin ziyarar tasu ta yini uku, za su je jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya domin tattaunawa da sojojin da suka ji rauni da iyalansu.
Za kuma su kai ziyara zuwa jihar Legas.
Rundunar sojin Najeriya sun ce ziyarar ta wanda ya assasa wasan Invictus da ake shiryawa domin ƴan mazan jiya da sojojin da suka ji rauni a filin daga, za ta taimaka wa sojojin da suka ji rauni sanadiyyar aiki.
Najeriya dai na neman ta karɓi baƙuncin gasar ta Invictus Games a 2029.
Meghan kuma za ta jagoranci wani taron mata a shugabanci.
Ofishin jakadancin Birtaniya a Abuja ya ce ba shi da hannu a ziyarar ta Meghan da Harry saboda ma’auratan na ziyarar ne a ƙashin kansu.