Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya ce, ya na kan hanyarsa ta zuwa Amurka, inda zai gana da shugaban kasar Joe Biden.
Wannan ce tafiyarsa ta farko da zai yi tun bayan da Rasha ta fara mamaya a kasarsa a watan Fabairun da ya wuce.
Fadar gwamnatin Amurka ta tabbatar da ziyarar ta Mr Zelensky, ta na mai cewa za a ba wa Ukraine baturan makamai masu linzami don kara kare kasar daga hare haren Rasha.
Mr Zelensky dai na yawan karbar bakuncin shugabannin kasashen waje a Kyiv, sannan kuma ya na kai wa dakarunsa da ke sassan kasar ziyara akai-akai.
Amurka ita ce kasar da ta fi ba wa Ukraine taimakon makamai don mayar wa da Rasha martani.
Ana kuma ganin wannan ziyara za ta kara dankon dangantaka tsakanin Amurka da Ukraine.