Stephanie Frappart ce, za ta yi alkalancin wasa mai muhimmanci a gasar cin kofin duniya da za a yi tsakanin Jamus da Costa Rica, inda za ta zama mace ta farko da za ta jagoranci wasa a gasar ta maza cikin shekaru 92 da a ke fafatawa.
Frappart za ta kasance a tsakiya a karawar rukunin E a filin wasa na Al Bayt ranar Alhamis, wanda har yanzu kasashen biyu za su iya tsallakewa zuwa matakin gaba a Qatar.
Ta kasance daya daga cikin alkalan wasa uku mata da aka zaba a matsayin wani bangare na gasar cin kofin duniya a watan Mayu, tare da Salima Mukansanga ta Rwanda da Yoshimi Yamashita ta Japan.
Frappart dai ba bakon abu bane wajen kafa tarihi a wasan na kasa da kasa, kasancewar ta mace ta farko da ta jagoranci wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya na maza a watan Maris din 2021 tsakanin Netherlands da Latvia.
Alkaliyar ta Faransa ta kuma taba yin alkalancin wasanni da suka shahara a matakin kungiyoyi a baya, ciki har da gasar cin kofin UEFA Super Cup na shekarar 2019 tsakanin Chelsea da Liverpool, kuma bayan shekara guda ta zama alkalancin mace ta farko a gasar cin kofin zakarun Turai, inda ta jagoranci wasan Juventus. da Dynamo Kyiv.
Gaba dayan tawagar alƙalan wasan za su kasance mata, tare da Frappart tare da mataimakan Neuza Back da Karen Diaz.


