fidelitybank

A karo na farko ƙungiyar farar hula a Edo sun yi wa Tinubu zanga-zanga a kan fetur

Date:

Ƙungiyoyin farar hula a Edo, sun hau kan titunan Benin, babban birnin jihar, domin nuna adawa da karin farashin man fetur da aka yi a baya-bayan nan.

Kafar talabijin ta Channels ta ruwaito cewa, masu zanga-zangar sun bi ta wasu manyan tituna suna yin Allah-wadai da karin da kuma tsadar rayuwa a Najeriya.

Masu zanga-zangar dai sun ce abin na ci musu tuwo a kwarya inda suka soki matakin karin farashin man fetur yayin da ake fama da tsantsar talauci.

Masu zanga-zangar na dauke ne da kwalaye masu rubuce-rubuce daban-daban, sun kuma yi watsi da shirin tallafin Naira 8,000 da Gwamnatin Tarayya ke yi shirin yi bayan cire tallafin man fetur ɗin.

Zanga-zangar ta zo ne makonni bayan da shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana cewa an cire tallafin mai. Tun bayan nan kuma farashin kaya da man fetur suke hauhawa a fadin kasar.

Yayin da gwamnatin tarayya ke cewa matakin an dauka ne don ci gaban kasa, masu suka na ganin zai jefa kasar cikin mawuyacin hali.

A ci gaba da daukar wannan mataki, gwamnatin tarayya ta bayar da shawarar bayar da tallafin Naira 8,000 ga ‘yan Najeriya amma daga baya ta ce za ta sake duba lamarin bayan sukar da shirin ya sha.

Gwamnati ta yi kira ga ƴan Najeriya su yi hakuri kuma ta ce ana daukar matakan rage radadin cire tallafin.

the sun newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Kare Ya Kashe Ragon Layya: Mai ƙwacen waya ya kashe Sojin ruwa a Kaduna

Wani mai ƙwacen waya ya kashe wani soja bayan...

Sojoji sun hallaka ƴan Boko Haram da dama

Da sanyin safiyar ranar Litinin, dakarun rundunar Haɗin kai...

Tarzomar kama baƙin haure a Amurka na yamutsa hazo

An shiga rana ta uku a tarzomar da ake...

Alhazai sun kammala aikin Hajji bana

A ranar Lahadin da ta gabata ne alhazai miliyan...

Tinubu gyaran ƙasa za ka mayar da kai ba zaɓen 2027 ba – ACF

Ƙungiyar Tuntuɓar Juna ta Arewacin Najeriya, ta yi kira...

Ƴan Jagaliya sun caka wa Matashi kuwa lokacin da ya zo karɓar naman Sallah a Kano

Matashi Ibrahim Mahmud ya rasu sakamakon caka masa wuƙa...

Kallo Ya Koma Sama: Elon Musk zai fuskanci mummunar sakamako – Trump

Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka...

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...
X whatsapp