Rundunar ‘yan sandan jihar Kogi a ranar Lahadi, ta tabbatar da sake samun fashewar wani abu da har yanzu ba a tantance ba a garin Kabba da ke karamar hukumar Kabbah-Bunu a jihar Kogi.
Hakan na zuwa ne kasa da wata guda bayan faruwar irin wannan lamari a ranar 11 ga watan Mayu a wani gidan giya da ke kusa da Junction Lewu a cikin garin Kabba.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP William Ovye-Aya, wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin, ya ce ba a samu asarar rayuka ba.
Ovye-Aya ya bayyana cewa, fashewar ta faru ne a wata mashaya ta Omofemi dake Okepadi Quarters, Kabba, da misalin karfe 9:15 na yammacin Lahadi.
“Kamar yadda yake a yanzu, ba a samu asarar rai ba, sai dai kujeru da tebura da ginin da har yanzu ba a tantance yanayin fashewar ba.
“Tuni kwamishinan ‘yan sanda, Mista Edward Egbuka, ya umurci binciken mu na DC da kuma jami’an binciken Bam da su tashi zuwa wurin da lamarin ya afku domin sanin ainihin yanayin fashewar.