fidelitybank

A kalla mutane 20 ne suka mutu a zanga-zanga

Date:

Wani rahoto ya bayyana cewa, mutane ashirin ne suka rasa rayukansu sakamakon tarzoma da ta ɓarke a yayin gudanar da zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a ƙasar nan.

Rahoton wanda kamfanin Beacon Consulting, mai nazari kan tsaro ya fitar ya yi nuni da cewa an kashe mutanen ne a jihohi shida da ke faɗin ƙasar.

A cewar rahoton an samu ɓarkewar tarzoma ne a jihohi 10 da suka haɗa da Adamawa da Borno da Gombe, da Jigawa da Kaduna da Kano da Kebbi da Nasarawa da Neja da kuma Yobe.

Kamfanin ya ce jihohin da aka samu rashin rayuka sun haɗa da Neja inda aka kashe mutum shida, sai jihar Borno inda aka kashe mutum huɗu, da Kaduna inda mutum uku suka rasu.

An samu rahoton mutuwar mutane huɗu a Jihar Kano, inda aka kashe mutum ɗaya a Kebbi, sannan mutane biyu ne suka mutu a Jihar Jigawa.

Rahoton ya ƙarƙare da cewa jami’an tsaro sun gaza a yunƙurinsu na tabbatar da cewa zanga-zangar ta gudana ba tare da tashin hankali ba.

“Ranar farko ta zanga-zangar ta nuna cewa jami’an tsaro da jami’an gwamnati sun yi ƙoƙarin hana zanga-zangar ko kuma tabbatar da an yi ta cikin lumana amma hakan bai yi nasara ba sakamakon yawan Jama’a da suka fito zanga-zangar a jihohi da dama.”

Har yanzu dai hukumomi ba su fitar da alƙaluma a hukumance ba kan lamarin

legit nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp