Akalla mutum 11 ne suka mutu a ƙauyen Maikatako a gundumar Butura da ke yankin ƙaramar hukumar Bokkos da ke jihar, sakamakon harin da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai a jihar.
Rahotonni sun ce maharan sun je ƙauyen ne cikin dare inda suka riƙa harbi tare da cinnawa gidaje wuta,, lamarin da ya jikkata mutane da dama..
Kwamishinan yaɗa labaran jihar ya shaida wa BBC cewa rikicin ba na addini ko ƙabilanci ba ne, to amma ya ce rikicin ya yi kama da na manoma da makiyaya
Jihar Plateau na daga cikin jihohin da ake yawan samun tashe-tashen hankula masu alaƙa da ƙabilanci da addini a Najeriya.