Akalla mutane 10 ne suka mutu, wasu 19 kuma suka jikkata, bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai hari, a wani bikin al’adu da aka gudanar a al’ummar Chando Zerreci da ke masarautar Irigwe a karamar hukumar Bassa ta jihar Filato.
Sakataren Yada Labarai na Kasa, Kungiyar Matasan Irigwe, Lawrence Zango, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Lahadi.
Zango ya ce ‘yan bindigar sun kaddamar da harin ne a daren ranar Asabar, a lokacin bukukuwan al’ada na ‘Zerreci’, wanda galibi ke shigar da su sabuwar kakar noma.
Ya ce, wadanda suka jikkata a halin yanzu suna karbar kulawa a asibitin Enos da ke Miango, ya kuma yi kira ga gwamnati a dukkan matakai da hukumomin tsaro da su samar da mafita mai dorewa kan hare-haren da ake kai wa a kullum da ke janyo hasarar rayuka da dukiyoyi.