A safiyar ranar Litinin din da ta gabata ne wani bala’i ya afku a Masarautar Zuru ta Jihar Kebbi, biyo bayan kisan kiyashin da wasu ‘yan ta’adda suka yi wa wasu ‘yan kungiyar ‘yan banga su 65, wadanda aka fi sani da ‘Yan-Sa-Kai, wadanda suka yi wa kawanya a hanyar zuwa rumfarsu.
Wannan kisan kiyashi duk da dai ba shi ne irinsa na farko da aka yi a yankin ba, amma bisa ga dukkan alamu shi ne mafi muni, domin babu wani dan kungiyar ’yan banga da ya bi bayan ‘yan bindigar da ya tsere ya ba da labarin abin da ya faru a kauyen Makuku na karamar hukumar Danko/Wasagu.
Mambobin ’Yan-Sa-Kai da suka je aikin da ya yi sanadin mutuwarsu, ba wai daga al’ummomin masarautar Zuru ne kadai suka fito ba, har da ‘yan kabilar Magajiya da Danrangi da ke karamar hukumar Rijau ta Jihar Neja.
Mazauna kauyukan sun koka da yadda masu ba wa ‘yan fashin bayanai ke yi, inda suka ce, ya fallasa ‘yan ’Yan-Sa-Kai ga babban hatsari, kamar harin na baya-bayan nan.
Kamar dai harin da aka kai wa ‘yan kungiyar ‘Yan-Sa-Kai bai wadatar ba, sai ‘yan bindigar suka bude wuta kan rundunar bataliya ta 232 da ke Zuru a garin Kanya, lamarin da ya yi sanadin mutuwar jami’ai da sojojin Najeriya.
Mataimakin gwamnan jihar Kebbi Kanar Samaila Yombe (mai ritaya) na cikin rundunar da ‘yan ta’addan suka yi wa wuta. Ya kasance a yankin don tantance matakin aiwatar da aikin da sojojin suka yi.
Majiyoyi sun ce an yi musayar wuta mai tsanani a wajen garin Kanya tsakanin sojoji da ‘yan bindigar, kuma an samu asarar rayuka daga bangarorin biyu.
Duk da cewa babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnati kan adadin wadanda suka mutu, wata majiya ta bayyana cewa mataimakin gwamnan ya rasa kwamandan ayarinsa, ASP Idris Libata.