Masu zanga-zanga a jihar Oyo sun bi sahun masu zanga-zanga a fadin Najeriya domin nuna adawa da tabarbarewar al’amura a kasar.
Sun hallara a kan titin Iwo tun da safiyar yau Alhamis inda suke rike da allunan da ke daube da kokensu.
A jikin allunan an yi rubutu kamar “Dole mutane su yi nasara”, “A sove majalisar dattijai”, “A kawo karshen yunwa da wahalhalu yanzu”, da sauransu.
Bayan nan, akwai karin masu zanga-zangar da suka yi cincirindo a harabar jamio’ar Ibadan.
Masu shirya zanga-zangar sun shaida wa yan jarida cewa za su dunguma zuwa fadar gwamnatin jihar domin mika kokensu.
Yan sanda da saran jami’an tsaro suna shawagi a wuraren da masu zanga-zangar suka yi dafifi domin tabbatar da doka da oda.


