A yayin da ake fuskantar tabarbarewar wutar lantarki a fadin kasar nan, gwamnatin tarayya ta yi kira da a hukunta duk wanda ke da hannu wajen satar wutar lantarki ko lalata na’urorin wutar lantarki.
Gwamnati ta bayyana cewa tana aiwatar da matakan samar da daidaito a nan gaba tare da inganta rarraba wutar lantarki cikin gaggawa.
Da yake magana a wani taro da manyan jami’an hukumar a ma’aikatarsa, Ministan Wutar Lantarki, Cif Adebayo Adelabu ya bayyana karara ga Kamfanonin Rarraba (Discos) cewa kin yin lodi ba abu ne da za a amince da shi ba kuma zai iya sa a cire musu lasisi.
Adelabu ya yi gargadi ga Discos karara, yana mai cewa dole ne su shirya samar da wutar lantarki tsakanin kashi 90 zuwa 95 a yankunansu. Idan ba a yarda da su ba, za su fuskanci hukunci na tsari.
A yayin taron da ministan ya kira, wasu hukumomin da suka halarci taron sun hada da Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC), Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki ta Najeriya (TCN), Nigerian Bulk Electricity Trading Plc (NBET), da Hukumar Raya Wutar Lantarki (REA).
Adelabu ya kara da cewa gwamnati na iya neman Discos su kara jarin su, wanda za a saka a cikin takardar manufofin da ke fitowa kafin karshen Maris. Ya jaddada cewa dole ne Discos su kawo karin kudi don bunkasa ababen more rayuwa a fannin.